Jude

1Wasiƙa daga Yahuda, bawan Yesu Kiristi da kuma ɗanʼuwan Yaƙub,

Zuwa ga waɗanda aka kira, waɗanda Allah Uba yake ƙauna, waɗanda kuma Yesu Kiristi ya kiyaye.

2Jinƙai, salama da ƙauna su zama naku a yalwace.

Zunubi da Hallakar Marasa Tsoron Allah

3Abokaina ƙaunatattu, ko da yake na yi marmari ƙwarai in rubuta muku game da ceton nan namu, sai na ga ya dace in rubuta in gargaɗe ku ku tsaya da ƙarfi cikin bangaskiya wadda aka danƙa wa tsarkaka sau ɗaya tak. 4Gama waɗansu mutanen da aka rubuta hukuncinsu tun dā, sun shigo cikinku a ɓoye. Marasa tsoron Allah ne, waɗanda suka mai da alherin Allahnmu ya zama dalilin yin fasikanci suna kuma mūsun Yesu Kiristi makaɗaici Mai Iko Duka da kuma Ubangijinmu.

5Ko da yake kun riga kun san duk wannan, ina so in tuna muku cewa Ubangiji ya ceci mutanensa daga Masar, sai dai daga baya ya hallaka waɗanda ba su gaskata ba. 6Malaʼikun da ba su riƙe matsayinsu na iko ba amma suka bar gidansu kuwa-waɗannan ne fa ya tsare a duhu, ɗaure da dawwamammun sarƙoƙi saboda hukunci a babbar Ranan nan. 7Haka ma, Sodom da Gomorra da kuma garuruwan da suke kewaye da su suka ba da kansu ga fasikanci da muguwar shaʼawar jiki. Sun zama misalin waɗanda suke shan hukuncin madawwamiyar wuta.

8Haka kuma dai, waɗannan masu mafarki suna ƙazantar da jikunansu, suna ƙin ikon masu mulki suna kuma ɓata sunan talikan sararin sama. 9Amma ko Mikaʼilu babban shugaban malaʼiku, saʼad da yake mūsu da Iblis game da gawar Musa, bai yi karambanin kawo zargin ɓatan suna a kansa ba, sai dai ya ce, “Ubangiji yǎ tsauta maka!” 10Duk da haka mutanen nan suna maganar banza a kan komene ne da ba su gane ba; kuma abubuwan da suka fahimta bisa ga jiki, kamar dabbobi marasa hankali-waɗannan abubuwa ne suke hallaka su.

11Kaitonsu! Sun kama hanyar Kayinu; sun ruga a guje garin neman riba zuwa cikin kuskuren Balam; an hallaka su cikin tawayen Kora.

12Waɗannan mutane kamar ƙazanta ce cikin bukukuwan ƙaunarku, suna ci tare da ku ba ko kunya-makiyayan da suke ciyar da kansu kawai. Su hadari ne da babu ruwa, wanda iska take kori; su itatuwan kaka ne marasa ʼyaʼya waɗanda aka tumɓuke suka mutu murus. 13Su raƙuman ruwan teku ne masu hauka, suna tumbatsa kumfar kunyarsu; su taurari ne masu yawo, waɗanda aka ajiye mugun duhu saboda su har abada.

14Enok, na bakwai daga Adamu, ya yi annabci game da waɗannan mutane cewa: “Duba, Ubangiji yana zuwa da dubbai bisan dubban tsarkakansa 15don yǎ yi wa kowa shariʼa, yǎ kuma hukunta duk marasa tsoron Allah game da dukan ayyukansu na rashin tsoron Allah da suka aikata ta hanyar rashin tsoron Allah, da kuma dukan baƙaƙen kalmomin da masu zunubi marasa tsoron Allah suka faɗa game da shi.” 16Waɗannan mutane masu gunaguni da masu ganin laifin waɗansu; suna bin mugayen shaʼawace-shaʼawacen kansu, suna taƙama game da kansu suna kuma yin wa waɗansu fadanci domin riban kansu.

Kira don Jimiri

17Amma ku abokaina ƙaunatattu, ku tuna da abin da manzannin Ubangijinmu Yesu Kiristi suka rigyafaɗi. 18Sun ce muku, “A kwanakin ƙarshe za a kasance da masu baʼa waɗanda za su bi shaʼawace-shaʼawacensu na rashin tsoron Allah.” 19Waɗannan mutanen ne, suke raba ku, su ne masu bin abin da jiki ya faɗa kuma ba su da Ruhu.

20Amma ku, abokaina ƙaunatattu, ku gina kanku cikin bangaskiyarku mafi tsarki, ku kuma yi adduʼa cikin Ruhu Mai Tsarki. 21Ku zauna cikin ƙaunar Allah yayinda kuke jira jinƙan Ubangijinmu Yesu Kiristi don yǎ kawo ku ga rai madawwami.

22Ku ji tausayin waɗanda suke shakka; 23ku fizge waɗansu daga wuta ku cece su; waɗansu kuma ku ji tausayinsu, haɗe da tsoro-kuna ƙyamar ko tufafin da aka ɓata ta wurin ƙazantar jiki.

Yabo

24A gare shi wanda yake da iko yǎ tsare ku daga fāɗuwa yǎ kuma miƙa ku a gaban ɗaukakarsa marasa laifi da matuƙar farin ciki—  25ga Allah makaɗaici Ubangijinmu bari ɗaukaka, daraja, iko da mulki, su tabbata a gare shi, ta wurin Yesu Kiristi Ubangijinmu, tun filʼazal, yanzu da har abada abadin! Amin.

Copyright information for HauSRK